Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai, ta bayyana tsohon kocin Feyernood Arne Slot a matsayin wanda zai maye gurbin Jurgen Klopp.
Klopp ya bar kungiyar ta Anfield bayan shafe shekaru 9, inda ya lashe manyan kofuna da suka hada da gasar Zakarun Turai, Firimiya Lig da UEFA Super Cup.
- Ba Zan Taba Mantawa Da Liverpool A Rayuwata Ba – Jurgen Klopp
- Majalisar Ministocin Iran Ta Shiga Taron Gaggawa Bayan Mutuwar Shugaban Ƙasar
Arne Slot ya lashe babbar gasar kwallon kafa ta kasar Holland tareda Feyernood kafin ya amince zai koma Liverpool a karshen kakar wasa ta bana domin maye gurbin Jurgen Klopp.
Liverpool ta kare a mataki na Uku akan teburin gasar Firimiya Lig da maki 82 a bayan Arsenal da Manchester City wadda ta lashe kofin.