An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta kafofi daban daban sau miliyan 459, karuwar kaso 30 kan na bara. Kana an kalli liyafar ta talabijin har sau miliyan 189, karuwar kaso 12 idan aka kwatanta da bara. Baya ga haka, kallon liyafar kai tsaye ta kafofin zamani, ya kai sau miliyan 270, karuwar kaso 47 idan aka kwatanta da bara.
A bangaren kasashen waje kuwa, kafar yada labarai ta CGTN wadda ke karkashin CMG, ta tallata tare da watsa rahotanni masu alaka da liyafar cikin harsuna 82, haka kuma tashar CCTV ta watsa shirye shiryen liyafar masu ban sha’awa ga kafofin yada labarai na duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)