Idan aka ambato kalmomin Dankon Zumunci, to mutane da dama za su tuna da kasashen Sin da Serbia. A da, aminan biyu sun nuna yadda suke girmama juna, da amincewa da juna, da hadin kansu don samun nasara tare. A yanzu kuma, ta yaya kasashen biyu za su kara bunkasa dankon zumunci a tsakaninsu, bisa sabon yanayin da ake ciki? An samu amsa a cikin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wa Serbia daga ranar 7 zuwa 8 ga wata.
Yayin da Shugaba Xi ya ziyarci Serbia shekaru 8 da suka gabata, shugabannin kasashen biyu sun tsai da kudurin daga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, zuwa dangantakar abokantaka daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. A wannan karo kuma, shugabannin kasashen biyu sun sanar da cewa, za a inganta, da kyautata irin wannan dangantaka a kokarin raya makomar bai daya ta sabon zamani a tsakanin Sin da Serbia.
Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun bayar da sanarwar hadin kai don gudanar da ayyuka daga dukkan fannoni. Kasar Serbia kuwa, ta zama kasa ta farko a nahiyar Turai da ta amince da raya makomar bai daya tare da kasar Sin. Lamarin da ya shaida muhimmancin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da babban matsayin dangantakar ta musamman. (Kande Gao)