An ayyana Mista Daniel Asama na jam’iyyar Labour Party (LP), a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Jos ta Arewa/Bassa a tarayya da aka yi ranar Asabar.
Baturen zaben na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa James Damen, ne ya bayyana sakamakon zaben da safiyar ranar Litinin.
- Daliban Jami’ar Jos 6 Da Aka Sace Sun Shaki Iskar ‘Yanci
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Daliban Jami’ar Jos 7
Damen ya ce Asama ya samu kuri’u 66,422 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Adam Alkali na jam’iyyar PRP, wanda ya samu kuri’u 61,670.
Baturen zaben ya bayyana Ibrahim Hassan na jam’iyyar APC ya zo na uku da kuri’u 10,063.
Damen ya ce “Bayan samun kuri’u mafi inganci da aka kada da cika sharuddan doka, an ayyana Mista Daniel Asama a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Jos ta Arewa/Bassa a zaben Cike-gurbi,” in ji Damen.
Sakamakon, kamar yadda Baturen zaben ya sanar, ya nuna cewa Asama ya yi nasara a karamar hukumar Bassa ta jihar, yayin da Alkali ya yi nasara a karamar hukumar Jos ta Arewa.