Mahukunta a lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin, sun ce girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta auku a gundumar Luding ta hallaka mutane 46.
Mataimakin darakta a ofishin lura da ayyukan gaggawa na lardin Wang Feng ya ce, girgizar kasar ta auku ne a jiya Litinin, kuma baya ga wadanda aka tabbatar da rasuwarsu, ibtila’in ya sabbaba jikkatar sama da mutane 50, yayin da wasu 16 suka bace.
Mahukuntan lardin sun ce an shiga aiki gadan gadan, domin shawo kan ibtila’in, inda ya zuwa karfe 6 na yammacin jiya Litinin, masu aikin ceto sama da 6,500, da jirage masu saukar ungulu 4, da jirage marasa matuka 2 sun isa wurin domin gaggauta aikin ceton al’umma.
Masu aikin jinya daga cibiyar kula da lafiya ta Moxi, da sauran kauyuka da garuruwa makwanfa, sun gaggauta isa wurin da girgizar kasar ta auku, inda ya zuwa karfe 8 na dare, sama da wadanda suka jikkata 50 suka samu kulawar jami’an jinya dake wurin.
Kaza lika ya zuwa yanzu, rukunin ’yan sandan musamman dake aiki a wurin, sun yi nasarar ceto sama da mutum 30, da suka makale cikin baraguzan gine gine.
Bugu da kari, ma’aikatar kudi, da ma’aikatar ayyukan gaggawa, sun ware kudin Sin yuan miliyan 50, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 7.25, domin tallafawa ayyukan ceto da ba da agajin gaggawa. Ita ma gwamnatin lardin ta fitar da kudin Sin yuan miliyan 50, domin tallafawa yankin Ganzi na lardin na Sichuan.
Tuni aka samar da kayayyakin jin kai da suka hada da sama da tantuna 3,000, da gadajen tafi da gidan ka 10,000 ga gundumar Luding, inda ibtila’in ya fi kamari. (Saminu Alhassan)