Aƙalla ma’aikatan jihar Kaduna 5,000 ne suka fara rubuta jarabawar tabbatar da aiki ta hanyar amafani da kwamfuta (CBT) bayan shafe shekaru biyu da fara aiki.
Jarrabawar wacce ake sa ran za ta ɗauki tsawon kwanaki uku ana gudanar da ita a shiyya Uku da ke jihar, shiyya ta 2 ce ta fi yawan masu zana Jarrabawar da mutane 3,000, yayin da shiyyoyi ta 1 da 3 ke da mutane 1,000 a kowacce.
Shugabar hukumar ma’aikatan gwamnatin jihar Kaduna, Jummai Bako, wadda ta bayyana gamsuwarta da yadda ake gudanar da jarrabawar CBTn ba tare da wata matsala ba, ta bayyana cewa, jarabawar tana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da ma’aikatan gwamnati a ma’aikatan jihar.
Bako wacce ta bayyana hakan bayan ta duba ɗaya daga cikin cibiyoyin CBT, ta ce, ana gudanar da jarrabawar a cibiyoyi uku da aka keɓe, da suka haɗa da Jami’ar Jihar Kaduna a shiyya ta 2), Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Zariya (Shiyya ta 1) da Jami’ar Jihar Kaduna ta Kafanchan (shiyya ta 3).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp