A kalla ma’aikatan kiwon lafiya 83 na jihar Katsina ne ‘yan fashin daji suka yi garkuwa da su a cikin shekaru takwas da suka wuce kamar yadda shugaban kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya ta kasa
(MHWUN), Kwamared Mannir Mohammed Suleiman, ya shaida.
Ya shaida hakan ne a lokacin liyafar cin abinci da aka shirya domin karrama Dakta Shamsuddeen Yahaya dangane da samun mukamin babban sakatare mai cikakken iko na hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Katsina.
Suleiman ya ce, wadannan garkuwan sun faru ne a tsakanin shekarar 2015 zuwa wannan shekarar da muke ciki, ya kara da cewa 65 daga cikinsu an sake su bayan biyan kudaden fansa, yayin da kuma ma’aikatan jinya su 16 aka kashe bayan garkuwa da su a tsawon wannan lokacin.
Kungiyar ta ce, akwai kuma wani ma’aikaci daya da ya tsere da harbin bindiga a jikinsa, sannan akwai kuma wani mutum daya da har yanzu tsawon shekara hudu ba a same shi ba, inda ya bace bat.
Shugaban don haka ya bukaci gwamnatin jihar da ta sake bibiya da nazartar walwalar ma’aikatan jinya a jihar musamman wadanda suke aiki a kananan hukumomin da ‘yan bindiga ke kai hare-haren nan.
Ya taya sabon babban sakataren murnar samun wannan mukamin na shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko, ya nuna cewa da kwarin guiwa da gwamnan yake da shi wajen nada shi, tabbas zai iya kula da ofishin da aka ba shi.
Shi kuma a nasa bangaren, sabon babban sakataren ya roki goyon bayan kungiyar domin ya samu nasarar cimma burin kyautata harkokin kiwon lafiya a matakin farko.