Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da aiwatar da kashi 70 cikin 100 na tsarin albashi na CONPCASS/CONTEDISS na shekarar 2024 ga ma’aikatan manyan makarantun jihar, daga Oktoba 2025.
Gwamnatin ta ce amincewar na daga cikin kudirin gwamnatin Gwamna Sani na inganta jin dadin ma’aikata da kuma farfado da fannin ilimi a fadin jihar.
- Sauya Sheƙa: APC Za Ta Lashe Kashi 95% Na Ƙuri’un Kaduna A 2027 – Gwamna Sani
- Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar
Gwamnatin ta ci gaba da cewa, amincewar ta biyo bayan wani babban taro da gwamnan ya yi da shugabannin kungiyar hadin gwiwar manyan makarantu (JUTIKS), wanda ya kai ga dakatar da yajin aikin na tsawon wata guda da kungiyoyin suka tsunduma.
Tattaunawar wacce aka gudanar a gidan gwamnati dake Kaduna, kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, da majalisar jihar Kaduna karkashin jagorancin Kwamared Ayuba Suleiman ne ta dauki nauyin gudanar da taron, kuma wakilan kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun ilimi na kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli, Zariya; Kwalejin Ilimi, Gidan Waya; da kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta jihar Kaduna dake da cibiyoyin karatu a Kaduna, Kafanchan, da Pambegua, duk sun samu halartar taron.
Kungiyoyin sun ayyana daukar wani mataki na yajin aiki ne a ranar 30 ga Satumba, 2025, kan batutuwan da suka shafi aiwatar da tsarin albashi na CONPCASS/CONTEDISS na 2009, fa’idodin ritaya, da jin dadin ma’aikata gaba daya a manyan makarantu mallakar Jihar.