Annobar COVID-19 ta yi mummunan tasiri ga fannin yawon bude ido na kasa da kasa ciki har da kasar Sin. Kwanaki kadan da suka gabata, an yi hasashen farfadowar fannin hidimomin yawon shakatawa na Sin, inda aka yi hasashen saurin bunkasar sa a shekarar bana, ta yadda sashen zai amfani daukacin fannin yawon shakatawa na duniya baki daya.
Game da hakan, kakakin ma’aikatar cinikayyar ta Sin Shu Jueting, ta bayyana a Alhamis din nan cewa, Sin a shirye take ta yi aiki da dukkanin sassa, wajen samar da kyakkyawan yanayin musayar al’ummun ta da na sauran kasashen duniya bisa tsaro, da kiyaye lafiya, da tsari. Kaza lika Sin za ta ba da muhimmiyar gudummawa, wajen ingiza ci gaban fannin yawon bude ido, da farfadowar tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)