Kafafen yada labaran kasa da kasa da dama na ganin cewa, yadda al’ummar kasar Sin suka more hutun “ranar 1 ga watan Mayu”, wato ranar ma’aikata ta duniya, ya shaida babban karfin da tattalin arzikin kasar ke da shi, kana, albishiri ne ga murmurewar tattalin arzikin duk fadin duniya baki daya.
Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta jaddada a yau Alhamis cewa, karfin tattalin arzikin kasar ta zai ci gaba da taimakawa sosai ga farfadowar tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)