Game da kalaman sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da suka shafi yankin Taiwan na kasar Sin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta jaddada a yau Talata cewa, batun Taiwan, batu ne na cikin gidan kasar Sin, kana, babbar moriyar kasa ce mai matukar muhimmanci, kuma tushen siyasa ne na dangantakar Sin da Amurka, kana, tamkar jan layi ne na farko tsakanin su, wanda bai kamata a tsallaka ba.
Mao ta ce, Amurka ta yi alkawarin siyasa a bayyane kuma a fili kan batun yankin Taiwan. Amma tun da dadewa, Amurka ta yi biris har ta jirkita gaskiyar tarihi, da aikata kura-kurai a kan batun Taiwan, da sassauta shingen da aka kafa tsakanin mu’amalar ta da Taiwan, da yunkurin inganta alakar aikin soja da Taiwan, da hura wutar rikicin dake cewa, wai “Ukraine a yau, Taiwan a gobe”, har ma kafafen yada labarai suna cewa, gwamnatin Amurka ta tsara shirin murkushe Taiwan. Tambaya a nan ita ce: Meye ainihin makasudin Amurka? (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp