Yau Litinin 27 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labarai, game da halartar shugaban kasa Xi Jinping, bikin bude taron ministoci karo na 10 na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Deng Li ya amsa tambayoyin manema labaran.
Jami’in ya ce, taron zai maida hankali kan zurfafa tattaunawa a fannoni daban-daban, ciki har da tabbatar da aiwatar da matsayar shugabannin kasashen a zahirance, da fadada hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa a bangarori daban-daban, da gaggauta gina al’ummomin Sin da kasashen Larabawa masu kyakkyawar makoma ta bai daya, tare da nazartar matakai na zahiri. Kaza lika, za’a zartas da wasu takardu da dama game da sakamakon taron, al’amarin da zai karfafa samun fahimtar juna tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, da tsara ayyukan da za’a gudanar a nan gaba, tare kuma da bayyana ra’ayi iri daya na bangarorin biyu kan batun da ya shafi Palesdinu. A ranar 30 ga watan Mayun da muke ciki, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, tare da shugabannin wasu kasashen Larabawa hudu wadanda za su kawo ziyara kasar Sin, ciki har da sarkin kasar Bahrain, Hamad bin Isa Al Khalifa, da shugaban Masar, Abdel Fattah El-Sisi, da shugaban kasar Tunisiya, Kais Saied, da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, za su halarci bikin kaddamar da taron, tare da gabatar da jawabi.
Deng Li ya jaddada cewa, ci gaban dangantakar kasar Sin da kasashen Larabawan na haifar da alfanu ga al’ummomin bangarorin biyu, kuma za ta taimaka sosai ga wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya, da tabbatar da zaman karko a duk fadin duniya. (Murtala Zhang)