Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labaru a jiya Talata, don gabatar da yadda ake tallafawa samun ci gaban cinikin waje.
An bullo da sabbin matakai guda shida da nufin “daidaita cinikin waje”, ciki har da cinikayya ta intanet ta kasa da kasa da dai sauransu.
Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Wang Shouwen ya bayyana cewa, duk da rashin tabbas iri-iri da ake fuskkanta, amma har yanzu harkokin cinikayyar waje na kasar Sin na da kwarin gwiwa wajen samun bunkasuwa yadda ya kamata a cikin rabin karshe na shekarar da muke ciki.
Wang Shouwen ya bayyana cewa, a cikin watanni 8 na farkon bana, yawan kayayyakin shige da fice na kasar Sin ya kai RMB yuan triliyan 27.3, wanda ya karu da kashi 10.1 cikin 100 bisa na makamancin lokacin bara, cinikayyar waje ta kasar Sin, ta sake nuna alamar juriya da kuzari.
Kwanan nan, majalisar gudanarwar kasar ta duba tare da zartas da manufofi da dama don tallafa wa samun ci gaban cinikayyar waje yadda ya kamata, wadanda suka shafi fannoni guda uku, wato inganta karfin cinikin waje a fannin tabbatar da yarjejeniyoyi, da kara kuzari a fannin yin kirkire-kirkire, da kuma karfafa karfin ba da tabbaci.
A wannan rana kuma, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta ba da wasu hakikanan matakai guda 6, don karfafawa kamfanoni gwiwar shiga cikin bukukuwan baje koli daban-daban don samun oda, da cimma nasarar shirya baje kolin kayayyakin dake shiga da fita daga kasar Sin karo na 132 (Canton Fair), da kuma inganta taka rawar dandamalin yin kirkire-kirkire na cinikayyar waje da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)