A yayin taron manema labarai na yau da kullum da ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta gudanar a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar, He Yongqian ya bayyana cewa, kara harajin kwastam da Amurka ta yi wa kasarsa a ranar 1 ga watan Fabrairu ya saba wa ka’idojin WTO. A ranar 4 ga watan Fabrairu ne kasar Sin ta gabatar da kara ga tsarin sasanta rikici na WTO, kuma daga baya za a warware sabanin bisa ka’idojin WTO.
Dangane da karin harajin kashi 25 cikin dari da Amurka ta yi kan karafa da goran ruwa da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, He Yongqian ya ce, abun da Amurka ta yi mataki ne na ra’ayin bangaranci. Kuma kasar Sin na bukatar Amurka da ta gyara kuskurenta.(Safiyah Ma)