Yau Jumma’a, wani babban jami’in ma’aikatar harkokin kudin kasar Sin ya yi bayani game da ziyarar ministar harkokin kudin kasar Amurka a kasar Sin.
Inda ya bayyana cewa, bisa mu’amalar da kasar Sin da kasar Amurka suka yi, ministar harkokin kudin kasar Amurka Janet Yellen ta fara ziyarar aiki a kasar Sin a ranar 6 ga wata, kuma za ta gama ziyararta a ranar 9 ga wata. Ya ce ziyararta a kasar Sin ta kasance muhimmin matakin karfafa mu’amalar dake tsakanin kasashen biyu a fannin sha’anin kudi, bisa ra’ayi bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a tsibirin Bali.
Jami’in ya kara da cewa, ainihin dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ita ce cimma moriyar juna, kuma, ba wanda zai cimma nasara cikin yakin ciniki ko shirin katse huldar cinikayya. A cewarsa, kasar Sin na fatan kasar Amurka za ta samar da yanayi mai kyau na raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a cimma moriyar juna yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)