Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya ce kasar Sin ta dauki matakan soji domin tsaron kai, bisa la’akari da yadda kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan, a ranar 2 ga wata.
A cewarsa, wannan yunkuri ne da ya saba da alkawarin Amurka na kin goyon bayan ‘yancin Taiwan, kuma takala ce ta siyasa mai tsanani ga kasar Sin, yana mai cewa, kasar Sin na adawa da kin lamuntar hakan.
Rundunar yankin gabashi ta runduanr ‘yantar da al’ummar kasar Sin PLA, ta shirya kai farmaki na hadin gwiwar sojoji, ta ruwa da kasa tare da iko da yankin sararin samaniyarta, da kuma wasu atisayen soja a teku da sararin samaniya, a kewayen tsibirin Taiwan, wanda ke zaman lahani ga kawancen Amurka da Taiwan. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)