Hukumar Kididdiga ta kasar Sin NBS ta bayyana a jiya Juma’a a birnin Beijing cewa, ma’aunin farashin samar da kayayyaki na kasar Sin wanda ya bincika farashin kayayyaki daga kofar masana’anta ya yi kasa da kashi 4.6 bisa 100 a shekara a watan Mayu.
Raguwar ta fadada da kashi 1 cikin dari daga bisani a watan Afrilu. A duk wata, PPI na kasar Sin ya ragu da kashi 0.9 bisa dari, a cewar ofishin.
Dong Lijuan, masaniyar kididdiga a NBS, ta danganta raguwar ga yadda farashin kayayyakin kasa da kasa ke yin kasa, da karancin bukatu a kasuwannin kayayyakin masana’antu na cikin gida da na waje, da kuma kara tushen kwatance da aka yi a daidai wannan lokacin a bara.
Alkaluman da aka fitar a ranar Juma’a sun kuma nuna binciken farashin kayayyakin masarufi na kasar Sin, wanda shi ne ainihin ma’aunin hauhawar farashin kayayyaki, ya karu da kashi 0.2 bisa dari a duk shekara a watan Mayu. (Yahaya)