Uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan a yammacin jiya Talata, ta sha shayi kuma ta tattauna da takwararta ta kasar Finland madam Suzanne Innes-Stubb wadda ta yi rakiyar shugaban Finland Alexander Stubb don ziyarar aiki a kasar Sin.
Yayin tattaunawarsu, Madam Peng ta ce, Sin da Finland na da dogon tarihi da dimbin al’adu, tana mai fatan kasashen biyu za su kara karfin hadin gwiwarsu a fannonin fasahohin al’adu, da wasannin motsa jiki kan kankara, da sauransu, da ma karfafa zumuncin al’ummunsu. A nata bangare, Madam Suzanne ta jinjinawa Madam Peng kan rawar da ta dade tana takawa a bangaren raya sha’anin mata da kananan yara a duniya, ta kuma bayyana niyyarta ta samar da karin gudunmowa ga kokarin kara dankon zumuncin kasashen biyu. (Amina Xu)