A yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa Litinin din nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi nuni da cewa, ‘yancin rayuwa shi ne mafi muhimmancin hakkin bil-Adama.
Kuma ko za a iya magance matsalar tashe-tashen hankali mai nasaba da harbin bindiga yadda ya kamata, da kare hakkin al’ummomin kananan kabilu, shi ne muhimmin ma’auni da kasashen duniya za su yi amfani da shi, wajen auna salon ‘yancin dan-Adam na demokiradiyar kasar Amurka. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp