Ministar ma’aikatar lafiya a kasar Uganda Jane Ruth Aceng, ta ce magungunan yaki da cutar zazzabin cizon sauro ko Malaria da kasar Sin ta tallafawa Uganda da su, wadanda kimar su ta kai dalar Amurka miliyan 1.1, za su yi matukar taimakawa kasar wajen yaki da annobar ciwon.
Ministar wadda ta bayyana godiya ga kasar Sin, ta ce a bara, Uganda ta sha fama da bazuwar ciwon na Malaria, wanda ya yadu zuwa kusan sama da rabin gundumomin kasar.
Uwar gida Aceng, ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a, bayan karbar magungunan, daga jakadan Sin a Uganda Zhang Lizhong, a babbar ma’ajiyar kayayyakin kiwon lafiya dake Kajjansi, gundumar tsakiyar Wakiso ta tsakiyar kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp