Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda za ku gyara mamanku bayan kun haihu:
Wasu matan daga sun yi haihuwa daya za ka ga mamansu ya zube, hakan yana damun maigida, sannan suma matan ba sa jin dadin hakan.
Abubuwan da za ku tanada:
Habbatussauda, Hulba, Alkama, Gyada, Ridi, Danyar Shinkafa, Busasshen Karas
Yadda za ku hada:
Duk ki daka su waje daya, ki rika damawa kunu da su, kina sha kamar sau biyu a rana. Bayan wani dan lokaci za ki ga abin mamaki da yardar Allah.
Gyaran mama
Tabbas matsalar mama tana da yawa domin za ka ga wasu matan mamansu ya kwanta ko ya koma dan kankani sakamakon shayarwa. To idan kina son ya taso ya yi kyau sai ku yi wannan hadin ku gani.
Abubuwan da za ku tanada:
Albasa madaidaiciya, zuma, garin gero, madara.
Yadda za ku hada:
Ku samu albasa madaidaiciya, ku yanyanka, sai ku saka a tukunya da ruwanku ya tafasa shi sosai har sai ruwan ya koma baki, sai ku juye ruwan ku samu zumar ku mai kyau, garin gero ludayi daya, madara ta gwangwani daya na ruwa sai ku juye
su kan ruwan tafasasshe albasa nan ki sha, amma fa karki bari ya kwana baki shanye ba. Wannan hadi ne da zai gyara miki mama.
Gyaran Mama
Idan ana so, mama yayi kyau, ya yi laushi da sulbi da girma, sai a yi wannan hadin:
Kayan da za ku tanada:
Aya, Gyada, Ayaba (plantain), Alkama, Madara:
Ki samu aya, Gyada Kyaba da Alkama sai madara, za ki wanke Ayarki sai ki hada da gyadarki ki markada su ki tace, dama kin yanyanka ayabarki busasshiya ta yi gari ki tankade sai ki rinka diban garin plantain din kina hadawa da ruwan Ayaba Gyadarki kina sa madara ta ruwa kina sha, zai gyara mama domin wannan hadi ne wanda sai kin sha mamaki.
Girman Mama ko cikowar mama:
Abubuwan da za ku tana da A Islamic Chemist domin a yi amfani da su su ne.
1 Hulba (Fenugreek) da man ta (oil). 2 Shammar (Fennel seeds)
Yadda za ku hada:
A samu ‘ya’yan Hulba da ‘ya’yan shammar a Islamic Chemist, sai a nike su, a dake su sosai, amma kowanne daban-daban, haka kuma za a iya samun garin nasu a Islamic Chemist, ba sai an sha wahalar daka ba, sai a debi cikin karamin cokalin shayi na garin Hulbar guda1 a zuba a kofi, sannan a debi garin shammar din shima cikin karamin cokali guda a hade su a kofi daya ( Hulba da shammar),sai a tafasa ruwan zafi idan ya tafasa sai a zuba cikin kofin maganin a motsa da cokali sosai, a rufe bakin kofin.
Idan ya yi minti 10 a rufe ya jika sai a tace da rariya a zuba zuma ga ruwan da aka tace a sha, sannan a rika shafa man Hulba akan maman da dare, a shafa man ya shiga fatar maman sosai, za’a yi hakan (yin shayi da shafa man Hulba) sau biyu (2) a rana – safe da dare har na tsawon wata daya, za’a ga cikakken sakamako bayan wannan lokaci da yardar Allah.
Daga zuwa wannan lokaci ko kafin lokacin mace za ta fara jin mamanta sun kara nauyi, wanda alamace na girma da suke karawa, kara girman mama ba abu bane dake faruwa cikin dare daya kamar yanda wasu ke tunani.
Don haka akwai bukatar hakuri kafin a ga sakamakon da ake bukata.
Man Hulba yana da amfani idan aka jure ana amfani da shi, yana da amfani biyu:
Na farko, yana sanya gudanar jini da kyau wajen mama wanda zai taimaka wajen inganta lafiyar mama da kyawun fatar mama, Na biyu, yana bude tsokokin mama yanda za su kara girma da karfin fata mai rike mama tsaye ba mai yawan taushi ba wanda ke sa mai sanya mama ya sunkuya saboda yawan taushi.