Watan Ramadan lokaci ne da ke tattaro ‘yan uwa da abokan arziki a cikin al’umma a fadin duniya domin karfafa soyayya tsakaninsu cikin ibada. Lokaci ne da masoya ke tattaruwa suna mu’amala tun daga lokacin da ake sahur zuwa lokacin buda baki ta hanyar rarraba abinci a tsakaninsu cikin jin dadi da annashuwa.
A wannan lokacin abin ya wuce abin da ake sawa a baka kawai, yana tattare da labarai tare da motso tunani na abubuwan da suka faru a tsakanin masoya tare da matso da juna kusa da kusa.
- Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan
- Ma’aikatar Ilimin Amurka Na Shirin Korar Ma’aikata 1,300
Wannan shi ne daga cikin labarin nan na sinadarin MAGGI ya fara gabatar da wasanne da aka yi wa lakabi da ‘Tales of Ramadan’.
Wasan na tare da jarumai da suka hada da Rekiate Ibrahim-AttahRekiya Attah, Ramadan Booth, Rabiu Rikadawa, da sauran jarumai. ‘MAGGI Tales of Ramadan’ yana kunshe da darussa masu kayatarwa da aka tsara na mako 6 wanda zai fara daga farkon watan Ramadan. A yayin kallon wasan za a fuskanci muhimman abin da zai karfafa soyayya a tsakanin al’umma. Wannan kuma abu ne da ake bukata a rayuwa.
A kowanne shafi na labarin zai fito da cikakken abubuwan da suke tattare da darussan watan Ramadan a tsakanin al’umma gaba daya musamman ganin yadda aka kama baki da rana har aka zo yin buda baki da kuma lokacin da yin sahur.
A jawabinta, shugabar vangaren kula da sarrafa MaGGI na kamfanin Nestlé Nigeria, Mrs Rahamatou Palm-Zakari ta bayyana cewa, “Ramadan lokaci ne na rarraba abin da aka mallaka cikin jin dadi da annashuwa a tsakanain al’umma, kuma mun fara wannan taarin ne fiye da shekara goma da suka wuce. Za kuma mu ci gaba da tallafa wa iyalai a cikin al’umma kamar yadda muka saba a baya
Mun kuma yi alkawarin tattaro mutane daga sassan kasa wuri daya, tabbas MAGGI ya yi imanin zaburar da mtane donm su nuna soyayya a tsakanin su musamman wanna lokaci na Ramadan.
MAGGI na daga cikin abubnwan alfarma da kamfanin Nestlé ke sarrafawa. Muna kuma alfahari da cewa al’umma dama har ma da wadanda ba a haifa yanzu za su ci gaba da amfana da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp