Allah ya yi wa mahaifiyar shugaban Hukumar KARATO na Jihar Kano, Baffa Babba DanAgundi rasuwa.
Mun sami labarin rasuwar marigayiyar Hajiya Hassana Babba DanAgundi, a shafin facebook na shugaban na Karota, Baffa Babba DanAgundi.
- Ganduje Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Usman Bala
- Allah Ya Yi Wa Babban Limamin Masallacin Garun Kura A Kano Rasuwa
Sanarwa ta ce, za a yi Jana’izar marigayiyar a yau Litinin 03/01/2022 da misalin karfe 10 na safi a gidan Babba DanAgundi da ke unguwar Dan Agundi filin wali.
Marigayiyar ta rasu ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Muna addu’ar Allah ya gafarta mata, ya kyauta namu zuwan.