A safiyar ranar Alhamis, bisa agogon kasar Hungary, mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping Madam Peng Liyuan, da rakiyar mai dakin shugaba Tamas Sulyok na kasar Hungary Zsuzsanna Nagy, sun yi ziyarar bude ido a cikin fadar Budavari Palota dake birnin Budapest na kasar Hungary, inda suka sha shayi tare.
Yayin da take hira da Malama Nagy, Peng Liyuan ta ce, kasar Hungary kasa ce mai kyan gani, da jama’a masu son baki. Akwai dimbin fannoni masu kama da juna a al’adun kasashen 2, abin da ya sanya al’ummun kasashen 2 ke kaunar juna, da aza harsashi mai karfi na raya zumuntar dake tsakanin bangarorin 2. Ban da haka, Peng ta bayyana fatanta na ganin zumuntar ta dore, da ci gaba da karfafa a nan gaba. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp