A ranar Talatar da ta gabata ce kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar wakilai (PAC), ya kaddamar da bincike kan zargin yin watsi da aikin hanyar Gidanwaya-Guaran Dutse-Waman Rafi-Saminaka-Kano a Jihar Kaduna wanda kudinsa ya kai naira biliyan 1.46.
Kwamitin ya yi rajistar korafe-korafen ne a yayin wani zaman bincike a ranar Talata, sa’ilin da yake tambayar babban sakataren ma’aikatar ayyuka ta tarayya, Dakta Yakubu Adam kan aikin.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- Horor Da Kasar Sin Take Tallafawa Ya Inganta Yaki Da Nakiyoyin Da Aka Binne A Somaliya
An yi zaman ne kan duba muhimman kadarori na kasa musamman hanyoyin da aka gina daga gwamnatin da ta shude.
Shugaban kwamitin majalisar wakilan, Bamidele Salam ya koka da cewa gwamnatin tarayya ta ciyo bashin kudin aikin ne.
“Bayanan da muka samu daga ofishin kula da basussuka sun nuna adadin hanyoyin har da rancen da gwamnatin tarayya ta karba.
“Amma dai, wata hanya ta musamman mai suna Gidanwaya-Guaran Dutse-Waman Rafi-Saminaka-Kano a Jihar Kaduna da ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta bayar da aikin hanyar tun a ranar 5 ga Oktoba, 2022, kan zunzurutun kudi hai na naira biliyan 1.461 da aka biya ga kamfanin ‘Messrs Jam Jam Dynamic Platform Limited’.
“Ya kamata a kammala wannan hanya cikin watanni 12, akwai zargin cewa kwangilar hanyar da aka bayar a shekarar 2022 ba a fara ba, kamar yadda muke magana a yanzu, kuma ma’aikatar ayyuka ta tarayya ta biya dukkan kudaden aikin ga dan kwangilar da abin ya shafa,” in ji shi.