Majalisar wakilai ta tarayya ta umarci a dakatar da karin kudin cire kudade ta na’urar ATM ga kwastomomi wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shirya yi. Majalisar ta ce karin kudin hada-hadar kudi ta na’urar ATM zai kara jefa jama’an kasa cikin matsin rayuwa ne kawai.
Majalisar ta ce bankuna suna kara samun kudade, kuma irin wadannan kare-karen cajin da ake kakaba wa mutane bai dace ba, wanda maimakon gyara kara jefa jama’a cikin damuwowi za su yi.
- Jami’in Sin: Ba Za A Lamunci Ayyukan ‘Yan Aware Na “Ballewar Taiwan” Ta Ko Wace Hanya Ba
- Na Cire Tallafin Mai Ne Domin Kare Makomar Matasan Nijeriya —Tinubu
Sannan a cewar majalisar karin zai kuma rage yawan hada-hadar kudade ta bankuna wanda zai kai ga jama’a musamman masu kananan karfi ajiye kudadensu a mararsu ko gidajensu wanda hakan ka iya zama matsala ko ma ta tsaron dukiyarsu ne.
Matsayar majalisar na zuwa ne bayan kudirin da Marcus Onobun ya gabatar a kwaryar majalisar ranar Talata.
Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar ya ce, CBN a cikin sabuwar takardar da ta fitar, ta yi nazari kan kudaden hada-hadar kudi na ATM da aka tanada a karkashin sashe na 10.7 na kundin tsarin CBN na karbar kudaden da bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da na banki ke yi.
Ya kara da cewa bisa sashin 10.7 da aka sake nazarinsa a 2019, ya rage cajin daga N65 zuwa N35 kan kowace hada-hada.
Sai dai ya bayyana cewa za a biya Naira 100 ga duk wanda aka cire na Naira 20,000 ga kwastomomi daga wasu bankunan da ke yin mu’amala da ATM a harabar bankin.
Onobun ya jaddada cewa abokan hulda daga sauran bankunan da ke yin mu’amala da ATMs a wajen harabar bankin, manyan kantuna, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a, za a rika biyan su Naira 100 da karin N500.
Majalisar a cikin kudurorin ta ta bukaci CBN da ya gaggauta dakatar da aiwatar da wannan manufa, har sai an yi huldar da ta dace da kwamitocin da suka dace kan harkokin banki, kudi, da cibiyoyin hada-hadar kudi.
Ta koka da cewa tuni ‘yan Nijeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki da dama, da suka hada da hauhawar farashin kayayyaki, karin farashin man fetur, karin kudin wutar lantarki, da yawan kudaden banki da na hidima da ke rage yawan kudaden shiga da ake iya kashewa da kuma yin illa ga tattalin arzikin ‘yan kasa.
‘Yan majalisar sun ce aikin gwamnati ya hada da kare ‘yan kasa daga ayyukan cin hanci da rashawa da ka iya haifar da kara tabarbarewar tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp