Majalisar Wakilai ta umurci kwamitinta mai kula da harkokin man fetur da ya binciki kiran da aka yi na korar Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), Farouk Ahmed, bisa abin da ta kira da kalaman cin fuska ga matatun man fetur na Nijeriya.
Wannan dai ya biyo bayan amincewa da kudiri kan “Bukatar gaggawar magance kalaman rashin da’a da shugaban hukumar NMDPRA ya furta, wanda dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Oredo na jihar Edo, Hon. Esosa Iyawe, a zauren majalisa a ranar Talata ya jagoranta.
- ACF Ta Koka Da Rashin Tsaro, Talauci A Arewa
- Majalisa Ta Amince N70,000 A Matsayin Sabon Mafi Karancin Albashi
A kudirin, Iyawe ya bayyana cewa, ingancin man fetur na iya tasiri kan aikin injin, don haka, dole ana bukatar dizal ko man fetur mai ƙarancin sulphur ga kowane nau’ikan inji a kamfanoni, masana’antar wutar lantarki, tankunan ajiya, jiragen ruwa da duk wani inji mai babban aiki. Bugu da kari, yawaitar sulfur acikin man fetur yana haifar da lalacewa ga injuna kuma yana taimakawa wajen gurbata iska.
Ya kuma yi nuni da cewa, la’akari da irin hadurran da ke tattare da sinadarin Sulphur, gwamnatocin duniya sun dauki matakin daidaita shi ta hanyar gindaya ka’idojin da ake bukatar rage yawan hayakin wannan sinadari, wanda ake sa ran masu samar da dizal za su bi.
Ya sanar da cewa, a kwanakin baya, Shugaban Hukumar NMDPRA, ya bayyana cewa, man dizal da matatar Dangote ke samarwa bai kai wanda ake shigowa da shi kasar nan ba, kuma man da Matatar Dangote ke da shi na da sinadarin sulfur mai yawa.
Da take kare kanta, matatar Dangote ta bukaci a yi gwajin kayayyakinsu, wanda ‘yan majalisar suka je matatar da kansu don tabbatar da ingancin kayayyakin da matatar ke tacewa. Sakamakon binciken ya musanta zargin da shugaban NMDPRA ya yi.
Don haka, Iyawe ya nuna damuwarsa kan zargin da ake wa hukumar NMDPRA na ba da lasisi ga wasu ‘yan kasuwa da ke shigo da dizal mai yawan gaske a Nijeriya kuma gurbatacce, wanda kuma amfani da irin wadannan kayayyakin na haifar da babbar illa ga lafiya da asarar kudi ga ‘yan Nijeriya.