A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta karɓi rahoto daga Kwamitinta na wucin gadi da ke binciken satar danyen mai a yankin Neja Delta, a daidai lokacin da wani bincike cewa, Nijeriya za ta iya asarar sama da dala biliyan 300 sakamakon satar danyen mai, rashin kula da masana’antu, da dai sauransu.
Kwamitin, wanda Sanata Ned Nwoko (Delta ta Arewa) ke jagoranta, an kafa shi a farkon wannan shekarar don binciken rahoton satar danyen mai da ake ci gaba da yi, da kuma hanyoyin fitar da man ba bisa ka’ida ba – abubuwan da aka dade ana zargin cewa, su suka haddasa Nijeriya ta gaza wajen cika ka’idojin fitar da ɗanyen mai na kungiyar OPEC.
Da yake gabatar da rahoton kwamitin wucin gadin, Nwoko ya bayyana cewa, kwamitin ya gano “abubuwan takaici da rashin daidaito a tsarin ma’auni da kuma rashin aiwatar da aiki” a cikin harkokin gudanar da ayyukan sarrafa man.
Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa.














