Majalisar dattawa ta tabbatar da Aminu Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar kidaya ta kasa (NPC), tare da Joseph Haruna Kigbu da Tonga Betara Bularafa a matsayin kwamishinonin hukumar.
Tabbatar da hakan ya biyo bayan gabatar da rahoton tantancewar da shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da al’amuran jama’a na kasa, Sanata Victor Umeh, ya gabatar a zaman majalisar a ranar Talata.
Umeh, wanda ke wakiltar Anambra ta tsakiya, ya shaida wa majalisar dattawa cewa an tantance wadanda aka nada yadda ya kamata kuma an tabbatar da cewa, sun dace da mukaman.
“Wadanda aka nada sun bayyana a gaban kwamitin don tantancewa a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025,” in ji shi. “Kwamitin bai samu koke ko korafe-korafe ba a kansu, sun nuna shiri da cancanta akan ayyukan da aka zabo su”.
Ya bayyana sunayen wadanda aka tantance a matsayin: “Aminu Yusuf (Jihar Neja) – Shugaba, Joseph Haruna Kigbu (Jihar Nasarawa) – Kwamishina, Tonga Betara Bularafa (jihar Yobe) – Kwamishina.