Majalisar dattawa za ta karbi jerin sunayen ministocin shugaban kasa Bola Tinubu da ake ta jiran tsammani nan da kwanaki biyu masu zuwa, inji shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Michael Opeyemi Bamidele.
Sanata Bamidele, wanda ya bayyana hakan a wajen taron lacca na bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kaddamar da littafinsa na ‘Diamond Jubilee’ a ranar Talata a Abuja, ya ce da safiyar yau (Talata) ne shugaba Tinubu ya fada masa da kansa a lokacin da ya buga masa waya domin taya shi murnar cika shekaru 60 da haihuwa.
Ya ce, shugaban ya kira shi ta wayar tarho da misalin karfe 10:03 na safe, inda yace masa, ba zai samu damar halartar bikin ranar haihuwarsa ba sabida shirin mika wa majalisar dattawa jerin sunayen ministoci nan da sa’o’i 48 masu zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp