Majalisar Dattawa ta maido da ranar tantance sabbin Shugabannin Sojoji zuwa Laraba, 29 ga Oktoba, inda ta soke shawarar da ta yanke a baya na gudanar da tantancewar a mako mai zuwa.
Sanarwar ta zo ne jim kadan bayan da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta wata wasika daga Shugaba Bola Tinubu yana neman a tabbatar da nadin sabon Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, da sabbin Shugabannin Sojoji a zaman majalisar na ranar Talata.
- Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
- An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato
Akpabio ya bayyana cewa, sauya shawarar ya zama dole domin bai wa sabbin shugabannin sojin damar fara aiki ba tare da bata lokaci ba.
Shugaba Tinubu, a cikin wasikarsa, ya ce, an yi nadin ne bisa tanadin Sashe na 18(1) na Dokar Sojojin Kasa, Cap A20, ta Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004.
Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da wannan bukatar don gaggawa kan tabbatar da daidaito mai inganci a cikin tsarin tsaron kasar.














