Majalisar Dattawa a zamanta ranar Alhamis ta tabbatar da nadin Hafsoshin Tsaron Nijeriya da shugaba Tinubu ya nada.
Tabbatar da Hafsoshin Tsaron ya biyo bayan amincewa da kudirin da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidela ya gabatar kan tabbatar da sunayen Hafsoshin Tsaron da shugaban kasa ya zaba.
- Tinubu Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar Da Nadin Sabbin Hafsoshin Tsaron Nijeriya
- Tinubu Ya Yi Ganawarsa Ta Farko Da Hafsoshin Tsaro
Hafsan hafsoshin da aka tabbatar sun hada da: Babban Hafsan Tsaro, Manjo-Janaral Christopher Musa da Babban Hafsan Soji, Manjo-Janaral Taoreed Lagbaja sai Babban Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral Emmanuel Ogalla sai Babban Hafsan Sojin Sama, AVM Hassan Abubakar.
Wanda aka nada a matsayin Babban Hafsan Sojin Sama, AVM Hassan Abubakar, ya ce zai tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasar nan, kamar yadda shugaban kasa ke buri.
Ya yaba da kokarin shugabannin sojojin sama na baya, amma ya ce akwai bukatar a kara kaimi.
Cikin wata wasika da Tinubu ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Sen. Godswill Akpabio, wadda ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, ya nemi amincewar majalisar da ta tabbatar da shugabannin hafsoshin, kamar yadda sashe na 18 (1) na dokar sojojin kasa ta 2004 ta tanada.