A ranar 10 ga watan Oktoban kowacce shekara, majalisar dinkin duniya ta ware don kula da Kiwon Lafiyar kwakwalwa da tunanin dan Adam, inda a sakon majalisar ta bayyana cewa, lafiyar kwakwalwa da tunani mai kyau yana ba dan Adam damar gudanar da rayuwa mai gamsarwa da ba da gudummawa sosai ga al’ummomi.
Majalisar ta bayyana takaicinta cewa, daya cikin mutane takwas a duniya na fama da matsalar lafiyar kwakwalwa, wanda hakan yafi kamari cikin ‘yan mata da matasa.
- NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2023
- Rikicin Falasdinu Da Isra’ila: Saudiyya Ta Dakatar Da Duk Wata Tattaunawa Da Isra’ila
Bugu da kari, Uku cikin mutane hudu da ke fama da matsalar kwakwalwa, ba su samun isashshiyar kulawa ko kuma babu kulawa ma kwata-kwata, kuma da yawa suna fuskantar kyama da wariya.
“Kiyaye Lafiyar kwakwalwa ba gata ba ce ta wane da wane, hakki ce ta duk dan adam – ya zama dole a kula da Lafiyar kwakwalwa a duk cikin al’ummatai da ke cikin fadin duniyarmu. Dole ne gwamnatoci su ba da kulawa don magani ga masu matsalar kwakwalwa da kuma kiyaye hakkinsu.
“Dole ne kuma a magance matsalar cin zarafi tare da karya duk wani shingen da ke hana mutane neman tallafi don magance matsalar kwakwalwa kuma dole ne mu magance tushen da ke haifar da matsalar kwakwalwa kamar talauci, wariya, tashin hankali da sauransu.
“A wannan rana ta kula da Kiwon Lafiyar Hankali ta Duniya, muna sake jaddada cewa, kiyaye lafiyar kwakwalwa, hakki ne kuma ‘yancin dan adam ne ba tare da nuna wata wariya ba, tare za mu gina duniya mafi koshin lafiya inda kowa zai yi alfahari da ita” inji sakataren majalisar