Majalisar dokoki ta kasa ta amince da jimillar Naira tiriliyan 54.9 a matsayin kasafin kudin shekarar 2025, inda ta amince da kara kudirin farko da Naira biliyan 700 daga Naira tiriliyan 54.2
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, tun da farko shugaban kasa Bola Tinubu ya rubutawa majalisar dokokin kasar, inda ya bukaci a kara kasafin kudi na farko daga naira tiriliyan 54.2 zuwa naira tiriliyan 54.9 saboda karin kudaden shiga da wasu manyan hukumomin gwamnati ke samu.
Amincewar kasafin kudin ya biyo bayan gabatar da rahotannin majalisar dattawa da kwamitocin majalisar wakilai kan kasafin kudi a zaman da aka yi ranar Alhamis.