A daren jiya Alhamis ne majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta fitar da wata sanarwa, inda ta yi maraba da yarjejeniyar fitar da avocado da kasar Sin, inda ta bayyana hakan a matsayin “shaidar dimbim alfanun BRICS ga kasashenta da dukkanin abokan huldarta”.
An kiyasta matsakaicin yawan avocado na shekaru uku a Afirka ta Kudu ya kai ton 139,400, kashi 45 cikin dari ana fitar da shi ne zuwa Turai, a cewar kungiyar masu noman avocado ta Afirka ta Kudu.
Sanarwar ta ce, dalilin bude kasuwar kasar Sin, kasar Afirka ta Kudu ta samu damar kara fadada noman avocado, wanda zai ba da gudummawa sosai wajen samar da ayyukan yi kai tsaye a gonaki, da kuma a samar da wasu damammakin a fakaice. (Yahaya)