Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani a karshen mako ya musanta yunkurin tsige gwamna Nasir El-Rufai da ake zargin Majalisar nayi.
Ya bayyana rahoton da ake cewa Majalisar na yunkurin tsige gwamnan a matsayin kanzon kurege.
Auren Dole: Daya Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Za Ta Angwance Da Dan Ta’adda
A wata sanarwa da ya fitar, Zailani ya ce rahoton shirin tsige Gwamna, ‘yan adawa ne da makiya kyakyawar alakar dake tsakanin bangaren majalisar dokoki da na zartaswa karkashin El-Rufai ke kokarin kunna wuta.
Zailani ya kara da cewa, bisa ga dukkan alamu ana kokarin haifar da rikici ne tsakanin majalisar dokoki da bangaren zartaswa domin a hana al’ummar jihar Kaduna samun ribar romon dimokuradiyyar da suke samu.
Shugaban majalisar ya ce kuma ba gaskiya ba ne cewa ‘yan majalisar dokokin jihar suna binciken yadda ake kashe kudaden gudanarwar ma’aikatun jihar da hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar.
A wani bangare na sanarwar, ta ce: “An jawo hankalin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna kan rahoton zargin yunkurin tsige Gwamna Nasir El-Rufai kan zargin cin hanci da rashawa da ke yawo a shafukan sada zumunta.” Kakakin Majalisa.