Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan rikicin masarautun Kano, Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta samar da sabuwar dokar kirkirar masauratu masu daraja ta biyu a jihar.
Sabuwar dokar sarakunan masu daraja ta biyu, wadanda za su yi aiki karkashin Sarki mai daraja ta daya, wadanda suka hada da masarautar Rano wadda ta kunshi kananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya, sai kuma masarautar Karaye wadda ta kunshi, Karaye da Rogo sai kuma masarautar Gaya wadda ta kunshi Gaya, Ajingi da Albasu.
- Gwamnatin Kano Ta Gabatar Da Sabbin Tuhume-tuhume Kan Ganduje Da Kwamishinansa
- Matsalar Karancin Abinci Za Ta Ƙare Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamnatin Tarayya
Kamar yadda bayanan sabbin masarautun ke nunawa, wata shaida ce dabke nuna wannan ci gaban zai haifar da gagarumar sarkakkiyar siyasa da al’adun Kano.
Abin jira a gani shi ne yadda hukunce-hukuncen kotunan da ke sauraron shari’un da ke gabansu da suka shafi sarakunan da ke nunawa juna yatsa a Jihar Kano.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne, babbar kotun Jihar Kano ta haramta wa Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan da aka rushe kiran kansu a matsayin sarakuna a jihar.