Majalisar Tarayyar Nijeriya ta sanar da dakatar da dukkan ayyukan dokoki domin girmama marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a birnin Landan na ƙasar Ingila.
A wata sanarwa da Sakataren Majalisar Tarayya, Kamoru Ogunlana, Esq., ya fitar wa manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana alhinin da shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai ke ciki dangane da rasuwar tsohon shugaban.
- Rasuwar Buhari: Gwamnatin Katsina Ta Ayyana Yau Litinin A Matsayin Ranar Hutun Aiki A Jihar
- Buhari Ɗan Kishin Ƙasa Ne — Tinubu
“A matsayin girmamawa ga tsohon shugaban ƙasa, an dakatar da duk wasu ayyukan Majalisar Tarayya nan take har zuwa ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025,” cewar sanarwar.
Sakataren ya ce Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai sun umurci dukkan ‘yan majalisar da su sauya tsarin aikace-aikacensu don su samu damar halartar jana’izar tsohon shugaban.
Majalisar ta kuma miƙa sakon ta’aziyya a madadin dukkan mambobinta da ma’aikata ga Gwamnatin Tarayya da al’ummar Nijeriya da Gwamnatin Jihar Katsina da iyalansa da dangi baki ɗaya.
“Shugaba Muhammadu Buhari zai kasance abin tunawa saboda kishinsa ga haɗin kan Nijeriya da gaskiyarsa,” sanarwar ta ƙara da cewa. ‘Yan majalisa sun yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp