Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi uku bisa zargin yin balaguro zuwa kasashen waje ba tare da neman izini daga bangaren zartarwa ko majalisar dokokin jihar ba.
Shugabannin da aka dakatar sun hada da Mubarak Ahmed, Rufa’i Sunusi da Umar Baffa na kananan hukumomin Birniwa, Gumel, da Yankwashi, wadanda aka ce sun tafi kasar Rwanda ba tare da izini ba.
- Ofishin Jakadancin Saudiyya A Nijeriya Ya Yi Bayani Kan Soke Bizar Fasinjojin Nijeriya
- ‘Yan Bindiga Sun Kone Gonakin Manoma 20 A Jihar Neja
Majalisar ta dauki matakin ne bayan shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi, Aminu Zakari Tsubut ya gabatar da bukatar dakatar da shugabannin.
Tsubut ya bayyana matakin da shugabannin suka dauka a matsayin rashin biyayya, wanda ya kamata a bincika kuma a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.
A halin da ake ciki, majalisar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye, Lawan Muhammad Dansure, da zai binciki lamarin tare da mika rahotonsa ga majalisar nan da makonni hudu domin ci gaba da daukar mataki.