Majalisar wakilai ta amince da Naira biliyan Niara 24, domin gyran filayen Jiragen sama da ke a jihohin Kebbi da Nasarawa, domin ta karbi ci gaba da kula da filayen.
Wannan ya biyo bayan dubi da kuma amincewa da rahoton kwamitin majalisar ya yi ne.
Kwamitin majalisar da ke kula da bayar da bashi da karbo bashi na majalisar wanda dan majalisar Hon. Abubakar Hassan Nalaraba na jami’iyyar APC daga jihar ,Nasarawa ya tabbatar da hakan a wani karamin zaman da kwamtin ya yi a ranar Alhamis da ta gabata.
A watan Mayu ne, shugaba Bola Tinubu, ya bukaci majalisar da ta amince da Naira biliyan 15 da kuma wata Naira biliyan tara domin gyran filayen Jiragen biyu na jihohin Kebbi da Nasarawa, domin karbar filayen Jiragen biyu daga gun gwamnatocin wadannan jihohin.
A cikin bukatar ta Tinubu, ya turawa majalisar ya bukaci da kirkiro shirin alfarma ga gwamnatocin jihohin Kebbi da Nasarawa, domin gyran filayen Jiragen da ke a jihohin da gwamnatin tarayya ta karbe su.
Da yake gabatar da rahoton Hon. Nalaraba ya yi kira ga majalisar data amince da rahoton kwamitin gyran filayen Jiragen biyu, duba da cewa, majalisar zartarwar kasar ta amince da hakan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp