Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da samar da abinci mai gina jiki da tattalinsa ya fara bincike kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 1.12 na shirin Ba da Lamuni na Anchors.
Har ila yau, binciken ya shafi yadda cibiyar NIRSAL’s ta raba Naira biliyan 215 na ayyukan noma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) shi ma ya raba Naira biliyan 3 ga kananan manoma 22, 120 ta shirin AVCF.
- An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana
- Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53
Da yake jawabi a zaman binciken, shugaban kwamitin Hon. Chike Okafor, ya bayyana damuwarsa cewa, a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi 24 da suka raba kudaden Anchors Borrowers, guda 9 ne kawai, ‘yan majalisar ke da masaniya kansu.
Okafor ya ce, daya daga cikin muhimman ayyukan kwamitin shi ne, tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen tallafi da hukumomin gwamnati da abin ya shafa suka yi a fannin samar da abinci da tattalinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp