Majalisar wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Amurka da ta dawo da tsohon tsarin bayar da Biza ga ‘yan Nijeriya, tana mai cewa, matakin zai iya gurgunta dangatakar difilomasiyya, tattalin arziki da kuma dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
A wani kudiri na gaggawa da aka amince da shi a ranar Talata, ‘yan majalisar sun yi Allah-wadai da matakin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta dauka a ranar 8 ga watan Yuli na rage tsawon wa’adin Biza ga ‘yan Nijeriya daga shekara biyar zuwa wata uku kacal.
- Wasu Mahara Sun Sake Kashe Mutum 14 A Wani Kauyen Jihar Filato
- Majalisa Ta Ba Wa Shugaban NNPCL Awa 24 Ya Bayyana Gabanta Ko Ta Sa A Kamo Shi
Matakin a cewar ‘yan malisan, wani sauyin siyasa ne na bai-daya da babu adalci a ciki, wanda kuma ka iya kawo matsala ga difilomasiyya.
Wanda ya jagoranci yunkurin, Hon. Muhammad Muktar, a madadin sauran da ke goyon bayan kudirin da suka hada da Hon. Jesse Okey-Joe Onuakalusi, Hon. Adefiranye Ayodele Festus, Hon. Atu Chimaobi Sam, da kuma Hon. Akiba Bassey Ekpenyong ya bayyana hakan a matsayin wata babbar barazana ga miliyoyin ‘yan Nijeriya masu bin doka da oda da ke tafiya zuwa Amurka, domin yin karatu, aiki, kasuwanci da kuma ziyartar ‘yan’uwa.
“Dole ne wannan majalisa ta tashi tsaye, domin kare ‘yan Nijeriya,” Muktar yana mai cewa; idan ba a kalubalanci wannan sabuwar manufa ba, za ta iya yin tasiri kwarai da gaske, musammam a kan harkokin kasuwanci, ilimi da kuma cudanya tsakanin kasashen waje.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp