Majalisar wakilai za ta bincike yadda ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama ta Kasa ta saida hannun jaririn wasu tashoshin Jiragen sama na kasa-da-kasa.
Wannan matakin na majalisar, ya biyo bayan kudurin da Hon. Kama Nkemkanma ya gabatar wa da majalisar a zamanta na yau Laraba.
Kama, a yayin da yake gabatar da wannan kudurin ya ce, manyan tashohin Jiragen saman da Nijeriya ke tunkahu da su, an sayar da hannun jarin su ne ga kamfanonin waje da amincewar majalisar zartarwa ta kasa da ta gabata, wanda ya ce, ba abi ka’ida wajen sayar da hannun jarin ba kamar yadda dokar kasa ta tanada.
A cewarsa, an sayar da hannun jarin ne kawai domin azurta wasu tsirarun ‘yan Nijeriya da kuma wasu kamfanonin waje wadanda suka kasance ‘yan kanzagi ga wasu ‘yan Nijeriya.
Ya bayyana cewa, manyan tashoshin Jiragen sama na kasa-da-kasa, kamar na Legas, Abuja, da Kano suna fama da kalubale sabida son zuciyar wasu marasa kishin kasa duk da kokarin da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa kamar EFCC da ICPC ke yi wajen magance matsalar.