Shugaban makarantar kangararrun yara ta gwamnatin tarayya da ke a anguwar Barnawa a Jihar Kaduna, Kwantirola Musa Dauda Doguwa ya bayyana cewa, a halin yanzu makarantar na matukar bukatar kujerun zaman dalibai.
Doguwa ya bayyana hakan ne a hirarsa da LEADERSHIP Hausa a Kaduna. Ya ce ya kamata al’umma su sani cewa wannan makaranta ce ta gyaran tarbiyar kan-gararrun yara.
- Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
- Bikin Sallah: Ministan Yaɗa Labarai Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Su Dawo Da Kyawawan Dabi’un Da Suka Jingine
A cewarsa, an kafa makarantar ce tun a 1962, amma wasu gine-ginan har yau ba a sake su ba tsawon shukaru fiye da 62, kuma makarantar ta yaye dalibai da da-ma.
Shugaban ya bayyana cewa, duk da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na kula da tafiyar da makarantar, musamman wajen samar da kujeru da gyaran wasu gine-gine da suka lalace, akwai kuma bukatar gwamnatocin jihohi suma su shigo don tallafa wa makarantar.
Ko da yake shugaban ya kara da cewa, marantar ta rubuta wa gwamnatin jihar wasika kan wannan bukatar ciki har da gyaran wani babban dakin taro na makarantar wanda iska ta lalata.
A cewarsa, hakkin kula da tarbiyar yara abu ne da ya rataya a wuyan kowanni mutum. Ya ce yaro guda daya ne zai addabi iyayensa da danginsa gaba daya, am-ma kuma an tattaro mana irin wadannan kangararrun yaran sama da 400, domin su gyara tarbiyyarsu na barin muyagun laifuka irinsu shaye-shaye da sace-sace da sauran abubuwan marasa kyau.