• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Makarantun Da Ba Ƙwararrun Malamai Za Su Rasa Zama Cibiyar Rubuta Jarrabawar NECO

by Shehu Yahaya
2 months ago
NECO

Gwamnatin tarayya yanzu ta shirya tsaf wajen ɗaukar mataki akan makarantun Sakandaren da basu da ƙwararrun Malamai a faɗin tarayya Nijeriya waɗanda basu da shaidar mallakar satifiket na cancantar damar koyarwa daga hukumar kula da lamurran Malaman makaranta ta ƙasa. Irin waɗannan makarantun da suk ɗauki irin Malaman da basu da satifiket na cancantar koyarwar daga hukumar daga yanzu za su rasa damar da ake basu ta zama cibiyar rubuta jarabawar (WAEC), (NECO),da sauran nau’oin jarabawa.

Gwamnatin tarayya tace irin irin waɗancan makarantun ba za’a amince masu su ci gaba da zama cibiyar rubuta jarabawa ba.

Wata takardar da aka turawa babban Rajistara na Hukumar kula da harkokin Malamai ta ƙasa, TRCN, daga ofishin Minisatan ilimi Dakta.Tunji Alausa “ Ma’aikatar ilimi ta bada umarnin cewar kamar yadda tsarin ilimin yake, wanda ake buƙatar, a samu bunƙasar ƙwarewa a aikin koyarwa na Malaman makaranta, daga yanzu duk wani lamarin daya shafi  amincewa da cancantar zama cibiyar rubuta nau’oin jarabawa na Makarantun  Sakandaren gwamnati da kuma na masu zaman kan su, wato WASSCE, NABTEB,  NECO, da kuma NBIAS, abin zai zama ƙarshin ikon hukumar kula da harkokin, Malaman makaranta ta ƙasa, ita zata yi wa makarantun cancancewa ta ko sun cancanta da zama cibiyar  rubuta jarabawa.”

  • Gwamna Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Kan Yadda Kano Ta Zarce Legas, Oyo A Sakamakon NECO Na 2025
  • Gwamnatin Tarayya Ba Ta Soke Jarabawar WAEC Da NECO Ba

Umarnin ya ci gaba da bayanin “,daga watan Maris 2027  WASSCE, Mayu 2027 NABTEB, Yuni 2027  NECO da Yuni 2027  SAISSCE, duk makarantar da ta kasance Malamanta ba suyi rajista ba,kuma basu lasin na koyarwa daga hukumar za a cire sunan makarantar daga kasancewa jibiyar rubuta jarabawa.”

Domin a samu hanya mafi sauƙi ta cimma burin muradin, “Malaman makaranta waɗanda basu  yi karatun digiri na ilimi ba wato education  a matsayin darasi a Jami’a, amma kuma sun samu ƙwarewa kan koyarwa a aji, da abin ya kai tsawon watanni goma sha biyu, an aba irin Malaman ƙwarin gwiwa na su yi rajista da hukumar kula da ilimin Malaman makaranta, kamar yadda sanarwar ta ƙara jaddadawa.

LABARAI MASU NASABA

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Tsarin ya ƙunshi na “ kwas na ƙwarewa kan lamarin koyarwa na gajeren lokaci wanda akan yi wata uku zuwa shida ne,  bayan haka ne waɗanda suka yi kwas ɗin ne za su cancanci yin rajista da hukumar , har su samu Lasin na amincewa da sun cancanta  su yi aikin koyarwa.”

Tsarin na ma’aikatar ilimin ya ƙara jan kunne na da akwai buƙatar tabbatar da cewaana amfani da shi tsarin dokar kamar yadda aka bayyna “a kuma samu dama ta wayar da kan duk masu ruwa da tsaki kan lamarin” a duk illahirin faɗin tarayyar Nijeriya”saboda kar abin ya kawo cikas na jarabawar da ta shafi ƴ aƴ an al’umma.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu
Ilimi

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

November 8, 2025
gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
Next Post
Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan 10.5 Sakamakon Rashin Cin Gajiyar Kashin Dabbobi

Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan 10.5 Sakamakon Rashin Cin Gajiyar Kashin Dabbobi

LABARAI MASU NASABA

Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.