Mutane kimanin miliyan 826, sun yi tafiye-tafiye domin yawon shakatawa a cikin kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 4.1 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2019. Yawan kudaden shiga da aka samu sakamakon harkokin yawon shakatawar ya kai Yuan biliyan 753 da miliyan 430, adadin da ya karu da kaso 1.5 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2019. Kaza lika kudaden shiga a fannin kallon fina-finan sinima ya zarce yuan biliyan 2.73. Fasinjojin da layin dogo ya yi jigila kuwa a fadin kasar sun wuce miliyan 160…
…A lokacin hutu na bikin tsakiyar kaka, da bikin murnar ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin da aka kammala ba da dadewa ba, an nuna yanayin wadata a kasuwar hada-hadar kayayyaki ta kasar Sin.
- Kazakhstan, Kasa Marar Ruwa Mafi Girma A Duniya, Tana Da Nata Hanyar Shiga Teku
- Sin Da Wasu Kasashe 80 Sun Yi Kira Da A Kyautata Tsare-tsaren Tallafawa Tsoffi
Ga al’ummar kasar Sin, bikin murnar ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar, na daya daga cikin muhimman bukukuwa a ko wace shekara. Jama’a sun saba cin gajiyar wannan dogon hutun da ba kasafai ake samun shi ba wajen tafiye-tafiye da sayayya, don haka ake kiran bikin da sunan “Makon Zinare”.
Wadatar da aka nuna a lokacin “Makon Zinare” na ranar kasa ta bana, wata muhimmiyar alama ce ta daidaitawa, da farfado da tattalin arzikin kasar Sin. A farkon rabin shekarar bana, yawan GDPn kasar Sin ya karu da kashi 5.5 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, wanda ya ci gaba da kasancewa kan gaba a tsakanin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya. Wani mai magana da yawun hukumar ba da lamuni ta duniya IMF, a kwanan nan ya bayyana cewa, an ga alamun daidaitar tattalin arzikin kasar Sin daga bayanan da aka samu a baya-bayan nan. Citigroup, Goldman Sachs, da sauran wasu cibiyoyin kasa da kasa sun kara hasashen su kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a duk shekarar.
A yanayin da ake ciki na rashin karfin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da kokarin ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. Kuma hakan zai kore surutan tabarbarewar tattalin arzikin kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)