Ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) reshen jami’ar jihar Gombe (GSU), ta bayyana tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, a yau Laraba kan abinda suka misalta da gazawar gwamnatin jihar wajen biyan bukatunsu.
Wannan dai shi ne karo na farko da malaman jami’ar suka fara yajin aikin cikin gida tun kafa jami’ar inda cikin jawabin Shugaban kungiyar ASUU – GSU, Suleiman Salihu Jauro, da Sakatarenta, Mustapha Shehu, suka danganta matakin da rashin aiwatar da yarjejeniyar aiki ta 2021 tsakanin ƙungiyar da gwamnatin Gombe kan ƙarin kuɗaɗen da za a yi wa ƙungiyar
- Gwamnatin Tarayya Ta Fara Tattauna Da ASUU Don Hana Su Shiga Yajin Aiki
- Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Al’ummar Borno Kan Ambaliyar Ruwa
Sauran batutuwan sun haɗa da rashin biyan alawus-alawus da rashin samar da asusu na horarwa don tallafawa malamai don karo karatu da rashin aiwatar da ƙarin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan da ma rashin aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma daga 2020 zuwa 2023.
Da suke karin haske, sun ce an amince da cewa gwamnatin jihar za ta biya zunzurutun kudi har Naira miliyan 10 a cikin kudin da ake rabawa jami’ar a kowane don ci gabanta, amma sun koka da yadda gwamnati ta biya kudin ne a watan Janairu da Fabrairu 2021.
A cewar kungiyar, rashin isasshen kudaden da gwamnatin jihar ke aika wa jami’ar ya sa take kasa a gwiwa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na gudanar da ayyuka wanda hakan ya tilasta mata bullo da ƙarban kudaden sashen kuma hakan yana dagula matsalolin kudi a kan dalibai.