Duk da koke-koken da masu ababen hawa da matafiya suke yi a kan gadar Namnai da ta rufta a kan babbar hanyar tarayya ta Jalingo-Wukari a jihar Taraba, ruwan sama mai karfi ya sake wanke wata hanyar da mutanen kauyen suka gina ta wucin gadi, lamarin da ya sa masu amfani da hanyar suka makale a gaɓar kogin Namnai a ranar Laraba.
Idan dai ba a manta ba, a kwanakin baya ne gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya ziyarci inda gadar Namnai ta rufta, inda ya ce gwamnatin jihar a shirye ta ke ta karɓe aikin sake gina gadar da ta rufta a hannun gwamnatin tarayya.
- Yadda Sabon Tsarin Harajin Kwastam Na Amurka Ke Shirin Gurgunta Tsarin Kasuwanci Na Duniya
- Trump Na Son Yin Wa’adi Na Uku Na Shugabancin Amurka
LEADERSHIP ta kuma tattaro cewa, gwamnatin jihar ta hannun ma’aikatar ayyuka ta bayar da kwangilar sake gina gadar ga Kamfanin gine-gine na Cloneburge akan kudi sama da Naira biliyan 19.
A lokacin da yake wurin, Kefas ya shaida wa masu ababen hawa da matafiya cewa, gwamnatin jihar za ta samar musu da wata hanyar da za su amfani da ita kafin a kammala gyaran gadar, alkawarin da har yanzun bai cika ba, ga kuma wani mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata, wanda ya wanke gadar wucin gadi da mutanen yankin suka gina a matsayin madadi.
Wakilin LEADERSHIP a wurin gadar da sanyin safiyar Larabar nan, ya gano cewa, hanyar wucin gadi da mazauna kauyen suka gina, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya wanke ta, lamarin da ya sa masu ababen hawa da matafiya suka makale a gaɓar kogin Namnai.
Wakilinmu ya kuma gano cewa, matasan yankin na dakon mutane da matafiya a bayansu domin tsallakawa da su ta cikin kogin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp