Danyan man da Nijeriya ke hakowa a kullaum ya karu zuwa ganga miliyan 1.35 a cikin watan Oktoba, a kokarinta na cimma muradin kungiyar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC).
Sai dai kuma, a wannanin da suka gabata danyan man da Nijeriya ke hakowa ya karu, wanda ya kai kasa da bukatar kungiyar OPEC. Wannan na kunshe ne a cikin rahoton kasuwar danyen mai na OPEC na watan Nuwambar 2023.
Babbar majiya da ta fito daga kasashe 13 da ke a cikin kungiyar OPEC ya nuna cewa, danyen man da aka hako ya kai ganga miliyan 27.90 a watan Oktobar 2023.
A cewar rahoton, hakar danyen mai na kasashen Angola, Iran da Nijeriya ya karu, inda kuma hakar danyen mai na kasashen Libiya, Saudiyya da Kuwait ya ragu.
Majiyar ta kara da cewa, Nijeriya ta hako danyen mai da ya kai ganga 1,416 a kawacce rana, inda kuma a wani kaulin aka bayyan cewa ta hako gangar da ya kai 1,351 a kowacce.
Bugu da kari, a wani rahoton da hukumar da ke sa ido a kan hako mai (NUPRC) ya bayyana cewa, Nijeriya ta hako gangar mai da ya kai jimlar miliyan 42 a watan Oktobar 2023. Wannan ya nuna kimanin danyen mai da aka hakowa ya karu daga miliyan 1.5 zuwa miliyan 40.4 a watan Satumba.
A kwanan baya ministan mai, Heineken Lokpobiri ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen kara hako danyen mai zuwa sama da ganga miliyan 2 a kullum.
Sai dai, ya sanar da cewa satar mai da fasa bututun mai su ne manyan kalubalen da ke shafar cimma wannan buri. Ya ce gwamnatin tarayya na kan kokarin kawo karshen wannan kalubale a bangaren hakar man fetur a kasar nan.