A ci gaba da sauye-sauyen wurin aiki da sabon babban hafsan sojan Nijeriya (COAS), Manjo Janar Taoreed A. Lagbaja, ke yi wa hafsoshin soji, Manjo Janar John O. Ochai ya zama kwamandan Kwalejin sojojin Nijeriya na 32 (NDA) da ke Kaduna a ranar Litinin, 26 ga Yuni, 2023.
Ya karbi ragamar shugabancin ne daga hannun Manjo Janar Ibrahim M. Yusuf, wanda ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 33 akan aiki.
A takaitaccen jawabinsa yayin taron mika ragamar shugabancin da aka yi a hedikwatar NDA, Manjo Janar Yusuf, ya gode wa Allah da ya ba shi nasara ya zama daya daga cikin wadanda suka rike ragamar shugabancin Kwalejin ta NDA.
Ya kuma yabawa daukacin al’ummar Kwalejin bisa irin goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake rike da shugabancin Kwalejin, ya kuma bukace su da su ba wa magajinsa hadin kai, wanda ya bayyana shi a matsayin babban jami’i kuma wanda ya dace da mukamin.
Shima da yake jawabi a wajen taron, sabon Kwamandan NDAn ya bayyana nadin nasa a matsayin wata dama ce da ya samu ta yin aiki, inda ya bayyana cewa, babban nauyin da ya rataya a wuyansa shi ne kula da daliban Kwalejin da kuma inganta jin dadin ma’aikatan Kwalejin.
Ya sake jinjinawa magabacinsa, Manjo janar Yusuf, inda ya bayyana shi a matsayin babban mutum kuma hafsan soja mai matukar nasara a rayuwa.